Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam - Manyan Lakcoci Apk
Apk Infos
Version | 2.9 |
Rating | 5.0/5, based on 6 votes |
Size | 73.1 MB |
Requires Android | Android 4.1+ (Jelly Bean) |
Author's Notes | Wannan app yana dauke da wasu zababun Manyan lekcoci SheikhJa'afar Mahmoud Adam |
About Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam - Manyan Lakcoci APK
Table Of Contents
Description
Assalamu Alaikum warahmatullah.Wannan app yana dauke da wasu zababun Manyan lectures ne guda hudu na SheikhJa'afar Mahmoud Adam, shine muka ga ya dace muyi application wanda mutane zasu su saurara a saukake.
Lectures din sune kamar haka:
-Gwagwarmaya - Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam
-Lakca akan Asalin Maulidi- Sheikh Jafar
-Tarihin Sheikh Jafar - Daga Bakinsa
-Wa'azin Karshe Na Sheikh Ja'afar Adam
Allah ya sakawa Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya kuma jikansa.
Domin samun sauran apps na sauran manyan malamai na sunnah duba ( rrnapps ) free Hausa Islamic apps dake cikin play store.
*Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam*
An haifi marigayi SheikhJa'afar Mahmoud Adam agarin Daura, a shekara ta 1962
(ko da yake wani lokacin yakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, awurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin
su, wanda kuma shi nemu sabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.
Tunkafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai
girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan
kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma
Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan. Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da take Sokoto. Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci balaga da adab a wajensa. Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar dasu, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai girma, Kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy. Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin cibiyar
(Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre). Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi. Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa. Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa.
Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan aljanna.
Latest updates
What's new in version 2.9
1.This Update includes bug fixes and improvements2. New version with some awesome features
How to install Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam - Manyan Lakcoci APK on Android phone or tablet?
Download Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam - Manyan Lakcoci APK file from ApkClean, then follow these steps:
Update Phone Settings
- Go to your phone Settings page
- Tap Security or Applications (varies with device)
- Check the Unknown Sources box
- Confirm with OK
Go to Downloads
- Open Downloads on your device by going to My Files or Files
- Tap the APK file you downloaded (com.andromo.dev658544.app670611-v2.9-ApkClean.apk)
- Tap Install when prompted, the APK file you downloaded will be installed on your device.
Older Versions
2.9 (1051) | 73.1 MB |
Questions & Answers
Q: What is an APK File?
A: Just like Windows (PC) systems use an .exe file for installing software, Android does the same. An APK file is the file format used for installing software on the Android operating system.
Q: If I install an APK from this website, will I be able to update the app from the Play Store?
A: Yes, absolutely. The Play Store installs APKs it downloads from Google's servers, and sideloading from a site like ApkClean.net goes through a very similar process, except you're the one performing the downloading and initiating the installation (sideloading).
As soon as the Play Store finds a version of the app newer than the one you've sideloaded, it will commence an update.
Q: Why ApkClean.net can guarantee APK 100% safe?
A: Whenever someone wants to download an APK file from ApkClean.net, we'll check the corresponding APK file on Google Play and allow user download it directly (of course, we'll cache it on our server). If the APK file does not exist on Google Play, we'll search it in our cache.
Q: What are Android App permissions?
A: Apps require access to certain systems within your device. When you install an application, you are notified of all of the permissions required to run that application.
Don't hesitate to contact us if you have any questions or concerns.
(*) is required